YAU SHEKARA 13 DA KASHE SHIEK JA'AFAR MAHMOUD ADAM KANO
An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a garin Daura, ranar 12 ga watan February 1960.
Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, a Wurin mijin Yayarsa, Mallam
Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza,
kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa Kano.
Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, Wanda
asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.
Tun kafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978.
Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980.
Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen
kasar Misra a cibiyar yada Al ' Adun Rude Misra, Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru
na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu.
Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu: Waccan makarantar ya je ta da Daddare Bayan Sallar Isha' in, waccan kuma ta koyo harshen
larabcin da yamma.
Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983.
Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988.
A shekara ta 1989,ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta
Ilimin Tafsir wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993.
Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar
Kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Kasa-Da-Kasa Ta Afrika da take Khartoum, Sudan.
Yana dawowa gida baiyi wata -wata ba yakama wa'azi,yakuma kafa cibiya maisuna USMAN BIN AFFAN. Cikin shekara ta 1995 wannan cibiyar ta shahara, kuma tazama wacce take cin gashinkanta, yana koyar dayawa karatun addini, duk watan Ramadhan yakanyi a garin Maduguri.
Har ila yau shine shugaban asusun wannan cibiya ta Usman Bin Affan. Yawakilci Najeriya a gasusukan kur'any alokuta daban -daban, yana Cikin kwamitin malamai na jihar Zamfara da Bauchi.
Sannan kuma, kafin Rasuwarsa,ya yi kokari wajen kammala karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir (Phd), a Jami ' ar usman dan Fodiyo da take Sokoto.
Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar,
Sheikh Abdul-Aziz Ali al- Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar dandago,wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa.
Akwai kuma Jibrin Abubakar Sheikh Limamin Masallacin Juma'a BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano.
Daga cikin malamansa na jami'a kuma, akwai Sheikh Abdurrafi'u da Dr. Khalid Assabt.
Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar da su, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai Girma, kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, ARB'UNA
Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam,
Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus salaatun Nabiiy.
Sannan kuma yana gudanar da karatuttuka a gidajen rediyo, da talabijin daban -daban. Kamar su rediyo, Kaduna, Bauchi ARTV Kano, DITV, Kaduna NTA, Borno, OITV Damaturu, NTA Yola.
Wasu daga cikin daliban Malam sun hada da Malam Rabi 'u Umar R /lemo da Malam Sani Abdullahi Alhamidi Dorayi da Mallam Abdullah Usman da Malam Usman Sani Haruna da Malam Ibrahim Abdullahi Sani Da Malam Yunus Ali Muhammad da Dr. Salisu Shehu da Malam Shehu Hamisu Kura da malam anas Muhammad Madabo.
Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wannan cibiya (SHIEK JA'AFAR ISLAMIC DOCUMENTATION CENTRE ).
Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428
(13/04/2007) kimanin karfe 5:30 na asubah. Alokacin yana jagorantar sallar asubah a babban masallacin jaumma'ar dake anguwar Dorayi. Wasune wadanda har yau din nan ba a gano su ba. Da makamai suka shigo har Cikin masallacin suka harbe shi. Sun same shine a kirjinsa da kuma wurin cibiyar Sa.
Anyi hanzarinwucewa dashi babban asibitin koyarwa na Aminu Kano, amma kafin likitoci su zo gare shi ya bar duniya.
Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa.
Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa, kuma
an binne shi ne a makabartar Dorayi.
Allah ya jikan sa, ya gafarta masa, ya yi masa tagomashi da gidan aljanna.
Amin.
Mukuma idan ta mu ta zo Allah ya sa mu cika da imani.
0 Comments