Subscribe Us

header ads

Covid 19: Za a rufe wasu kasuwanni a Kano



Gwamnatin jahar ta ce zata rufe wasu daga cikin kasuwannin da ke jahar tare da tsaurara hana shiga da fita a kan iyakokinta, bayan samun bullar cutar coronavirus a jihar ranar Asabar.

Gwmamnan Jahar Abdullahi Umar Ganduje ya shaidawa BBC cewar, tuni aka killace wanda ya kamu da cutar ta covid19 mai shekaru saba’in da haihuwa a asibitin Pfizer na kwanar Dawaki, inda gwamnatin jihar ta yi tanadi domin killace masu dauke da wannan cuta.

Gwamna Ganduje ya ce ya zama dole gwamnatin jahar ta dauki tsauraran matakai don hana cinkoson jama’a, duk da hakan zai iya takurawa al’ummar jahar.
A yanzu dai Kano ta zama jiha ta baya bayan nan da aka samu bullar cutar coronavirus, bayan bullar ta a makwabtan jihar Kaduna da Katsina.

Post a Comment

0 Comments