Subscribe Us

header ads

Ba Mu Da Wata Hujja Na Kin Yin Sallar Juma'a Idan Har Tsoro Bai Hana Mu Yin Harkokin Duniya Ba. Cewar Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaria


Kira ga Gwamnatin Kaduna game da dakatar da sallar Juma'a

Ya zama dole mu fito mu fadawa kanmu gaskiya, idan har gwamnati zata iya ba jama'a damar fitowa kasuwanni cikin cunkoso dan neman abinci a ranakun talata da laraba, ba tare da fargabar yaduwa cutar corornavirus ba, lallai akwai matukar bukatar a duba maganar dokar dakatar da sallar jummu'a, domin tsakani da Allah ba mu da wani hujja na barin sallar Juma'a idan har tsoro bai hana mu zuwa kasuwanni ba.

Muna kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta duba wannan lamarin, tayi koyi da sauran gwamnatocin jihohin Arewa kamar jihar Sokoto da Kano da Bauchi da Plateu wadanda suka samar da ka'idoji da tsarin da za'a bi dan kaucewa yaduwar cuta a lokacin gudanar da sallar jummu'a maimakon dakatar da sallan dungurun gun. Awa daya zuwa awa biyu ya isa a gudanar da sallar jummu'a.

Muna kira da tattausar murya ga gwamnatin jihar Kaduna da ta duba Allah ta dauke wannan dokar. Allah yasa mu dace amin.

~ Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaria
(Mataimakin Shugaban Kungiyan Fityanul Islam na kasa)

Post a Comment

0 Comments