Daga Bangis Yakawada
A cikin makon da ya gabata ne wata kungiya da ta yi ikirarin mazauna Zariya sun fitar da wata takarda mai dauke da koke masu yawan gaske kan shugaban cibiyar nazarin sinadarai ta kasa (NARICT) dake Basaw a karamar hukumar Sabon Garin Zariya ta jihar Kaduna.
Wakilinmu ya ziyarci cibiyar don jin gaskiyar maganar koken da kungiyar mara adireshi ta fitar akan shugaban
Daga cikin korafin akwai maganar shugaban Ma'aikatar Farfesa Jeffrey T. Barminas ya wuce ka'idar zama shugaba a cibiyar da sauran tuhume- tuhume masu yawa.
Hakan yasa wannan jarida ta ziyarci cibiyar don jin gaskiyar lamarin.
Malam Rabi'u Haladu, shi ne shugaban sashen bincike da tsare-tsare na cibiyar kuma ya yi karin haske game da lamarin, inda ya ce Babu wani kamshin gaskiya a takardar koken na su hasalima zuki ta mallace kawai, domin a batama shugaban Ma'aikatar suna, yace shugaban kasa ya san da zaman Farfesa Jeffrey T Barminas don shi ya kawo shi wannan cibiya don ya gwada bajintarsa don haka yana sane da komai nasa.
Malam Rabi'u ya kara da cewa makiya ne da marasa kishin cibiyar suke yin wannan rubuce-rubucen.
Karshe ya ce tuni cibiyar ta yi watsi da wannan kage da ake yi wa shugaban na su.
Kuma ya ce ya zuwa yanzu suna nazari akan lamarin don daukar matakin da ya dace.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin wadanda suka gudanar da koken amma bai sami dama ba bisa yadda wani rahoto ke nuna cewa hukumar 'yan sanda sun gayyace su don gudanar da binciken akan lamarin.
Kuma wannan ba sabon abu bane a wannan ma'aikata ta NARICT ZARIA, Domin batun yau ba ake samun bata gari suke rubuce rubuce da soke soke mara sa dalili domin ganin sun batama shugaban wannan ma'aikata Farfesa Barminas Jeffrey Tsware, suna a idanuwan Al'umma sedai kuma har yanzu hakar su bata cimma ruwa ba domin kuwa Al'umman wannan yanki suna nuna amincewar su da kuma nuna goyon baya ga shugaban Ma'aikatar ta NARICT
An zagaya da wakilin mu lunguna da sakon wannan ma'aikata domin ya tabbatar da ganema idon sa halin da Ma'aikatar take ciki, ya kuma tabbatar mana da irin cigaban da aka sama a Ma'aikatar
Naga samfuran injinan zamani na milyoyin naira a Ma'aikatar, kuma naga sabbin gine gine suma dai na zamani a Ma'aikatar wanda Farfesa Barminas Jeffrey Tsware, ya samar tun a lokacin hawan sa matsayin shugaban na Ma'aikatar
Ko a kwanain baya a ranar 20-01-2022, seda Karamin ministan Kimiyya da Fasaha da Kere-Kere ta kasa, (Barista, Muhammad H. Abdullahi) Ya Ziyarci Ma'aikatar Inda kuma yayi kwanaki biyu domin kaddamar da wasu muhimman aiyuka masu yawan gaske wadanda ma'aikatar ta kirkiresu a karkashin jagorancin Farfesa Barminas Jeffrey Tsware,
Shima kuma Uban kasa Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, bisa rakiyar 'yan Majalisar Masarautar Zazzau da Hakiman sa ya kai ziyara ta musamman zuwa Cibiyar ta Binciken Kimiyyya Sinadarai ta Kasa (NARICT)
Kuma Farfesa Jeffery T. Barminas da sauran mahukuntan Cibiyan suka zagaya da Mai Martaba Sarkin, zuwa wasu daga cikin wuraren Bincike da Gwaje-Gwaje na Cibiyar
Kafin ya kamalla wannan ziyara, Mai Martaba Sarkin Zazzau ya gabatar da jawabi ga Ma'aikata da Mahukuntan Cibiyan, inda ya jawo hankalinsu wajen bayar da hadin kai ga mahukuntan Cibiyan domin samun ci gaba da bunkasan Kasa, sannan kuma yayi gargadi ga masu yin shaidanci ga shugaban Ma'aikatar.
0 Comments