Wani sabon rikicin kabilanci da ya barke a jahar Taraba tsakanin kabilun Shomo da Jole dake karamar hukumar Lau ta jahar taraba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Daily Trust ta ruwaito a sakamakon rikicin, an kona garin Shomo Sarki gaba daya, kuma a nan ne aka fi samun asarar rayuka da dukiyoyi da yawa a yankin.
Rikicin ya samo asali ne a kan wata fadamar kamun kifi dake kusa da tafkin Benuwe, inda kabilun biyu suke zama, sakamakon tafkin ya ratsa ta cikin karamar hukumar Lau ta jahar.
Kuma ana yawan samun fadace fadace tsakaninsu, wadda yasa gwamnatin jahar a baya ta dakatar da dukkanin su daga amfani da fadamar wajen kamun kifi.
Amma a wannan karo, jama’an guda daga cikin kabilun ne suka yi kokarin karya dokar wajen shiga fadamar don kamun kifi, sai al'umar dayar kabilar ta hanata da karfin tuwo, daga nan rikici ya kaure.
Daruruwan mutane da suka hada da mata, tsofaffi da kananan yara sun tsere daga gidajen su.
Shi ma Kakakakin Yansandan jahar, David Misal ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace tuni rundunar ta tura mataimakin kwamshinan Yansanda don tabbatar da zaman lafiya a yankin.
“Mun samu labarin rikicin, kuma ya shafi mutane da dama, amma ba zamu iya fadin adadin wadanda aka kashe ba, amma mataimakin kwamishinan Yansanda ya isa garin don samar da zaman lafiya.” Inji shi.
0 Comments