Subscribe Us

header ads

Wasu mutum 11 sun kamu da coronavirus a jihar Legas




Gwamnatin Jihar Legas ta tabbatar da samun wasu mutum 11 da suka harbu da cutar Covid-19 a ranar Asabar 11 ga watan Afrilu, abin da ya kawo jumullar adadin zuwa 177 a jihar.

Kwamishinan Lafiya Farfesa Akin Abayomi ne ya bayyana hakan a yau Lahadi, inda ya ce wasu mutum hudu kuma sun warke har ma an sallame su daga cibiyar killacewa - jumullar adadin ya kama 50.

Abayomi ya ce an sake samun wani mutum da ya mutu sakamakon cutar kuma yawan wadanda suka mutu a jihar sun zama shida kenan.
Hukumar NCDC ta ce ya zuwa karfe 9:30 na daren Asabar, mutum 318 ne suka harbu da coronavirus a Najeriya, 70 sun warke sannan 10 sun mutu.

Post a Comment

0 Comments