Subscribe Us

header ads

CORONA VIRUS: Buhari Ya Amince Da Cire Dala Miliyan 150 Daga Asusun Nijeriya Na Musamman Don Yakar Coronavirus


CORONA VIRUS: Buhari Ya Amince Da Cire Dala Miliyan 150 Daga Asusun Nijeriya Na Musamman Don Yakar Coronavirus

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da cire dala miliyan 150, kimanin naira biliyan 55 daga asusun kasa na musamman wanda aka fi sani da suna ‘Sovereign Wealth Fund’ don yakar Coronavirus Kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

Buhari ya amince a cire kudin ne domin raba ma matakan gwamnatin tarayya, jahohi da kuma na kananan hukumomi sakamakon bullar annobar Coronavirus.

Ministar kudi, da tsare tsare, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka a yau A Abuja yayin da take ganawa da manema labaru game da matakan da gwamnati take dauka don rage radadin Coronavirus.

Ministar ta bayyana cewa za’a cire kudaden ne don cike gibin da aka samu sakamakon karyewar farashin gangar danyen mai a kasuwannin duniya.

Tace tun daga watan daya na shekarar bana kudaden shigar gwamnati ke yin kasa, wanda hakan ya shafi kudaden da ake rabawa tsakanin matakan Gwamnatoci.

Haka zalika gwamnatin Najeriya za ta nemi karin kudaden bashi daga bankin lamuni na duniya, IMF, bankin duniya da kuma bankin cigaban nahiyar Afirka domin kulawa da matsalolin tattalin arzikin da za’a fuskanta sakamakon Coronavirus.

Post a Comment

0 Comments