Babu Wurin Da Ya Kai Masallaci Albarka A Duniya, Kada Ku Hana Jama'a Zuwa Masallac, Sakon Sheikh Jingir, Ga Gwamnati
Shugaban Majalisar malamai na kasa na kungiyar Izalah Sheikh Sani Yahya Jingir ya e masallaci guri ne da mutane ke samun natsuwa da kwanciyar hankali saboda Manzon Allah S A W ya ce babu wasu mutane da za su taru a dakin Allah su karanta Alqur'ani da darusan addini face Allah ya saukar musu da nutsuwa a tare da su".
Sheikh Jingir ya yi kira da gwamnonin da suka kulle masallatai ya ce su bude a cigaba da darusan addini da ibada don samun rabauta duniya da lahira.
A karshe Sheikh Jingir ya yabawa shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamnan Filato Simon Lalong bisa matakan da suka dauka na bada kariya ga al'ummarsu ba tare da hana su ibardarsu ba.
Sheikh Jingir ya yi wannan bayani ne jiya Juma'a a yayin da yake gabatar da nasihar Juma'a a garin Jos kamar yadda ya saba a kowanne mako.
0 Comments