Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kori kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar, Muazu Magaji, saboda farin ciki da rasuwar Shugaban Ma’aikata fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kamar yadda Daily Nigeria ta ruwaito.
Idan ba zaku manta bakwamishinan ya rubuta a shafin sa na Facebook domin nuna farin cikin sa game da rasuwar shugaban ma’aikatan.
Wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba ta ce an cire kwamishinan ne bayan kalaman sa na murna ga mutuwar marigayi Abba Kyarin.
0 Comments