Subscribe Us

header ads

Coronavirus Ta Ruguza Kasafin Kudin 2020, Cewar Gwamnatin Nijeriya



Gwamnatin Tarayya ta yi wa dokar kasafin kudin 2020 kwaskwarima, ta yadda za ta fasa aiwatar da duk wasu dimbin ayyukan da ta Yi alkawarin yi, amma kuma a yanzu ta ke ganin yi wa al’ummar Najeriya wadannan ayyukan ba zai yiwu ba kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Hakan kuwa ya faru ne sanadiyyar yadda annobar Coronavirus da ta barke a duniya, ta haifar da mummunan matsalar karyewar tattalin arzikin kasashe.

Babban abin da matsalar ta fi shafa ta fannin tattalin arziki, shi ne farashin danyen man fetur a duniya, wanda ya karye har zuwa kasa da dalar Amurka 20.

Danyen man fetur shi ne babbar hanyar samun kudin shigar Najeriya, wanda ta shata kintacen kudin shigar da za ta aiwatar da kasafin 2020 a bisa farashin kowace gangar danyen mai dala 57.

Karyewar darajar danyen mai a duniya, ta sa Najeriya zaman zullumi da taraddadin yadda za ta bullo wa lamarin kasafin. A karshe dai ta yanke shawarar zabtare kaso mari yawa na kasafin wanda ta ce ba za ta iya aiwatarwa ba.

Har ila yau, Gwamnatin Tarayya ta zabtare kirdadon kasafin kudi daga dala 57 na farashin kowace gangar danyen mai, zuwa dala 30 kacal. Abin da a Rurance ake kira benchmark.

Ministar Harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ce ta bayyana cewa gwamnati ta sa gatarin yi wa kasafi sassabe, ta guntule duk wasu manyan rassan da ta san matsalar tattalin arziki da faduwar darajar danyen bai ba za su wadatar har a aiwatar da su ba.

Ta ce yanzu an shiga “mawuyacin halin da babu wani tsimi ko dabara, sai dai a fuskanci abin da zai yiwu kawai shi za a iya yi.”

Post a Comment

0 Comments