Shugaba Buhari zai dawo da 'yan Nijeriya mazauna kasar Chana.
Ofishin jakadancin Nijeriya da ke birnin Beijing a kasar China, ne ya fitar da sanarwar.
Ofishin ya ce, gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shirye domin fara jigilar 'yan kasar nan mazauna can domin dawo da su gida Nijeriya.
A cewar ofishin daukar wannan mataki ya biyo bayan fitar wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ya nuna yadda hukumomi a birnin Guangzhou suka fatattaki wasu ‘yan kasuwar kasar nan da dalibai da ke karatu a can kasar ta China daga dakunan Otal dinsu.
Rahotanni sun ce birnin Guangzhou shine gari da al’ummar Afirka suka fi ziyarta domin gudanar da harkokinsu na kasuwanci a kasar ta China.
Ofishiɓ yace sakamakon wannan abu da akewa yan Kasar Nigeria zata kwaso yan kasar ta daga Chinan.
0 Comments